Hajjin bana: CBN ya Amince da Baiwa Alhazai Guzurinsu a hannu ba ta ATM ba

Hajjin bana: CBN ya Amince da Baiwa Alhazai Guzurinsu a hannu ba ta ATM ba

 



Babban Bankin Kasa (CBN) ya amince da bukatar maniyyata ta a ba su guzirin su a hannu kamar yadda aka saba ba ta katin ATM ba.

Hakan ya biyo bayan magana da shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi, wanda ya roki shugaba Bola Ahmed Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

An dade ana fargabar cewa har yanzu amfani da katin ATM da CBN ya gabatar don gudanar da aikin hajji zai kawo hadari ga tsare-tsare, gudanar da ayyuka da gudanar da aikin Hajjin 2025.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da mataimakin shugaban hukumar, kwamishinan tsare-tsare da sarrafa ma’aikata da kudi na NAHCON, Aliu Abdulrazaq, ya tabbatar da cewa CBN ta bai wa maniyyatan Najeriya damar karbar guzirin su a hannu a tsabar kudi domin gudanar da ibadar  aikin Hajjin bana cikin sauki.

Post a Comment

Previous Post Next Post