Gwamnatin Kano ta Dakatar da Aikin Tsaftar Muhalli na Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB

Gwamnatin Kano ta Dakatar da Aikin Tsaftar Muhalli na Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB

 


Domin tabbatar da gudanar da jarabawar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun gaba da Sakandare (JAMB) ba tare da matsala ba, gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na karshen watan Afrilu.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da nazari tare da masu ruwa da tsaki, domin bai wa É—aliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata tangarda ba.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Isma’il Garba Gwammaja ya fitar, ya ambato Kwamishinan ma’aikatar na cewa:

“Dakatarwar tana da nufin kauce wa duk wata tangarda da ka iya hana gudanar da jarabawar yadda ya kamata, da kuma bai wa É—aliban da zasu yi jarabawar damar rubuta ta cikin kwanciyar hankali,” in ji Kwamishinan.


Published by: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post