Wannan shine kufan garin Sodom wanda Allah Ya Halakar da mutanen Annabi Ludu. Garin yana nan har yanzu babu kowa, sai alamun tokar wuta Garin yana kusa da ruwan Al-Lisan Turawa suna kiran sa "Dead Sea" akan iyakar kasar Jordan, tsallaken garin Falasdinawa, Girman garin a tsaye ya kai kilo mita sha hudu. da Akwai kissar a cikin Kur’ani (11:74–83 da 29:28–35) ko da yake ba a ambata sunayen garuruwan ba.
A Ranar 24 Ga Watan Satumba 2021 Masu Bincike Sun Gano Dalilin Rushewar Birnin Mutanen Annabi Ludu (A.S) Da Ke Yammacin Jordan masu bincike sun gano dalilin rushewar birnin mutanen Annabi Ludu da ke yammacin kasar Jordan.
masu gudanar da binciken wuraren tarihi sun gano dalilin rushewar birnin mutanen Annabi Ludu (A.S) wato Tel Hamam da ke yammacin kasar Jordan, Masu binciken sun ce wani dutse ne mai wuta da fadinsa ya kai mita 50, tsawonsa kuma ya kai kilo mita 4 ya fada kan birnin, wanda shi ne kuma ya rusa birnin da kona shi tun kimanin shekaru 3650 da suka gabata.
Haka nan kuma masu binciken sun ce, karfin tarwatsewar dutsen da kuma karfin saukarsa a kan kasa, ya ninka karfin fashewar bam din nukiliya wanda zai iya share birane Sau 44
Birnin Tel Hamam dai shi ne wurin da Annabi Ludu (A.S) ya rayu, wanda a lokacin ya ninka birnin Urshalim ko kuma Quds sau 10 a lokacin, wanda kuma shi ne birnin mafi girma a yammacin Sham, Daga cikin abin da masu binciken suka gano har da cewa, karfin zafin wutar da dutsen ya sauka da ita, a nan take ta sanya duk wani abu na karfe ko zaiba ko azurfa ya narke a nan take.
Wallahu A'alam.