Sana'ar Wanzanci a Kasar Hausa | Wanzamai

Sana'ar Wanzanci a Kasar Hausa | Wanzamai

 




wanzanci na da ga cikin sana'oin hausawa Wanda suke da tsohon usuli. sana'ar wanzanci, kowa na iya yi in har idan zai tsaya ya koya, amma yawanci masu yin ta a yanzu magada sun fi yawa, akwai sirri mai karfi da babban al'amari ga ma su yinta.

kuma su kan shahara a kan sana'ar ta su, ban da aski da yin kaho da cire beli, dayin kwalliya ko yin shash-shawa ga mai sha'awa ko yan gado. su kan taimaka da bada magunguna na gargajiya abisa lakaninsa, kuma da yardar Ubangiji akan dace.

Wanzamai suna da kayan aiki wanda suka hada da aska da kaho a cikin askar akwai ta bakin karfe da farin karfe da jan karfe, ko wacce askar da wanzamai sukan yi aiki da ita, sukan lakaba mata suna da sukan Kira ta dashi.

Misali akwai hinde, aska ce da ake yinta da bakin karfe wadda ake yin kaciya da ita, sai kuma bamasariya, wadda ake yinta da farin karfe don yin aski, sai kuma bintila wadda akeyi da bakin karfe, amfi anfani da ita wajen shash-shawa ko tsagar kaho, akwai kugiya ko koshiya abin cire beli, sai dutse abin washin wuka da kuma kaho wanda ake zukar jini da shi in an tsaga da aska sai uwa-uba zabira, wadda wata jaka ce da take dauke da duk kayayyakin da aka lissafa a sama.

Post a Comment

Previous Post Next Post