Babban limamin masallacin Juma’a na Baba mai Kasuwa, Tudun Wada Zaria, Sheikh Adamu Shu’aibu Adamu, ya shawarci maniyyatan jihar Kaduna da su gaggauta biyan kason farko na kudin aikin hajjin 2024.
A cikin hudubar sallar Juma’a ta jiya, Sheikh Adamu Shu’aibu ya bayyana cewa ajiye kudin aikin hajjin kafin karshen watan Disamba zai taimaka wa hukuma wajen yin kyakkyawan shiri da isassun shirye-shirye na aikin ha5jji ba tare da cikas ba.
Ya kuma jaddada bukatar masu hannu da shuni su biya kudadensu ta hannun hukumar da aka amince da su, Ya ce a baya-bayan nan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana cewa duk maniyyatan da ba su biya kudin aikin Hajji ba kafin karshen watan Disamba na iya rasa zuwa aikin Hajjin.
Sheikh Adamu Shu’aibu ya kuma bayyana bukatar da ke akwai ta musulmi su dukufa wajen gudanar da addu’o’i na yau da kullum domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen wahalhalu a fadin kasar nan, dangane da kalubalen da ake fama da shi a kasuwar canji a duniya.
A kwanakin baya ne Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta gudanar da wani gangamin wayar da kan Alhazai, inda ta nemi goyon bayan Limamai da Malaman Addinin Musulunci domin wayar da kan alhazai da sauran al’umma sabbin kalubalen da ake fuskanta na gudanar da aikin Hajji cikin nasara.