Waken suya nau'in wake ne mai launin rawaya ko (yellow) a turance wanda ake amfani da shi wurin yin madara, abincin dabbobi, awara da sauransu,
sannan Waken suya yana da matukar amfani ga lafiyan mutum ana kuma sarrafa shi ta hanyoyi daban daban, akan hada madara dashi a rinka ba jarirai kuma akan sarrafa shi izuwa abincin gargajiya da sauransu.
KADAN DAGA AMFANIN WAKEN SUYA
1. GINA JIKI
Waken soya yana da sinadari maigina jiki wato "Protein" Wannan sinadari yana da kyau kamar nama amma bashi da maiko kamar nama, Sannan bashi da "Cholesterol"
manya da yara da mata masu ciki da masu cutar qanjamau su yawaita cin waken Soya, ana kuma iya zuba cokalin na garin zogale a madarar waken soya kofi daya a sha.
2. YAWAN KITSE
Wannan kitse yayi yawa a jininsa ya
yawaita amfani da waken suya saboda yana da "Omega-3- fatty acide" mai rage yawan kitse a jini. Ana so mai yawan kitse ya yawaita amfani da waken soya dafaffe.
3. LAFIYAR KASHI
Akwai sinadarin "Calcium" a waken soya mai gina kashi da hakora, shi yasa ake baiwa yara masara mai launin rawaya domin tana da wannan sinadari.
RELATED:
• Amfanin Lemon Zaki Ga Lafiyar Dan Adam Da Kuma Sinadaren Dake Kunshe A Cikinsa
• Ko kasan Amfani Da Kanunfari Yana Jinkirta Tsufa Inji–Masana kiwon lafiya
• Amfani 5 Da Yayan Bagaruwa Da Ganyenta Keyi A Jikin Dan Adam
4. MAGANIN CIWON DAJI
Haka kuma waken soya yana taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da cutar ciwon dajin mama (Cancer) da hanji da Prostate masu cutar ciwon daji da masu son yin rigakafin kamuwa da cutar za su iya yawaita amfani da waken soya.
5. KARE ZUCIYA DA KODA
Masu ciwon suga suna da hatsarin
kamuwa da ciwon qoda da ciwon zuciya. masana sun gano cewa waken soya na da abubuwan da suke taimakawa wajen kare zuciya da qodar mai ciwon suga, mai wannan cuta ya yawaita amfani da waken soya.
6. INGANTA GARKUWAR JIKI
A cikin waken soya akwai sinadarin:
Magnesium, manganese, Copper,
Selenium da Vitamin B6, shi yasa yake taimako wajen inganta garkuwar jiki.
masu cutar qanjamau suma suna da
qarancin "selenium" mai son inganta
garkuwar jikinsa da na iyalinsa; su yawaita cin waken soya
7. MAGANIN BASIR (PILE)
Waken soya na da "Dietery fibre" mai
rigakafi da kuma maganin Basir mai cutar Basir ya yawaita cin waken soya amma dafaffe don yafi soyayye.
8. MATAN DA SUKA DAINA AL'ADA
Matan da suka daina al'ada saboda tsufa su yawaita cin waken soya zai taimaka wajen rage musu matsalolin dake zuwa da wannan larurar dakuma gina musu jiki.