Daga 2027, ƴan Nijeriya za su ƙara talauce wa - Bankin Duniya

Daga 2027, ƴan Nijeriya za su ƙara talauce wa - Bankin Duniya

 


VANGUARD ta rawaito cewa wannan na kunshe ne cikin rahoton taron da ke gudana tsakanin Bankin da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a Washington, Amurka.

Bankin Duniya ya yi duba cewa nan da 2027 talauci zai karu a Nijeriya da kashi 3.6 nan da shekaru biyar, farawa daga 2027.

Rahoton ya nuna mawuyacin hali da ƴan Nijeriya ke ciki duk da nasarorin habbakar tattalin arziki a kasar, musamman bangaren da ba na man fetur ba.

Sai dai kuma rahoton ya ce tsare-tsaren gwamnatin na gyaran tattalin arziki ya haifar da tsaiko wajen bunƙasar tattalin arziki a fadin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post