INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Fitacccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu a cikin daren da ya gabata, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar wa RFI Hausa. Majiyar ta ce za a gudanar da jana'izarsa a gobe Juma'a a garin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh.
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi wanda yayi shura wajen karantawa da tafsirin Al-qur'ani
Ubangiji Allah ya bawa sheikh tsawon rai na kusan ƙarni guda.
Muna Rokon Allah Ya jikansa da Rahama.
Ga Kaɗan daga cikin tarihin Sheikh Dahiru Usman Bauchi a taƙaice
Asali da haihuwa
Sunansa cikakke: Sheikh Dahiru Usman Bauchi (OFR).
An haife shi ne a 29 ga Yuni 1927, daidai da 1 Muharram 1346H, a yankin da yanzu ake kira Gombe/Bauchi (Konkiyel – Darazo, da kuma asalin mahaifiya daga Nafada, Gombe).
Bafulatani ne daga yankin tsohuwar jihar Bauchi.
Ilimi da karatu
Ya fara karatun Al-Qur’ani ne a wajen mahaifinsa, Alhaji Usman, ya haddace Qur’ani tun yana yaro.
Ya yi karatu a wajen manyan malamai kamar:
Sheikh Tijjani Usman Zangon-Bare-bari
Sheikh Abubakar Atiku
Sheikh Abdulqadir Zaria
Mahaifinsa muqaddam ne na Tijjaniyya, shi ma ya gaji wannan hanya ta dariqa.
Matsayinsa a addini
Yana daga cikin manyan shugabannin Dariqar Tijjaniyya a Najeriya, ana kiransa ma babban jagoran Tijjaniyya a Najeriya.
Yana Mazhabi Maliki, kuma Sufi ne (Tijjani).
Memba kuma mataimakin shugaban kwamitin Fatwa na Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA).
Aikin da ya fi shahara da shi
Ya shahara da:
Tafsirul Qur’ani a Hausa, musamman a watan Ramadan, wanda ake yadawa a rediyo, TV da social media.
Yawon wa’azi a jihohi dabam-dabam kan tauhidi, ibada, zaman lafiya da ɗorewar ɗabi’a.
Ana ɗaukar tafsirinsa a matsayin “Tafsir Sheikh Dahiru Bauchi”, daya daga cikin shahararrun tafsiran Hausa a arewacin Najeriya.
Kusa da Shehu Ibrahim Inyass
Sheikh Dahiru Bauchi babban mabiyi ne na Sheikh Ibrahim Niasse (Kaolack, Senegal).
Ya yi aure a cikin dangin Shehu Niasse; an ruwaito ya auri ɗiyar Sheikh Ibrahim Niasse, aure da aka ɗaura a masallacin Shehu a Senegal.
Ƙalubale da jarrabawa
A shekarar 2014, an kai harin bam ne a Kaduna a kan konvoinsa, yayin da ya ke kan hanya bayan wa’azi. Ya tsira, amma mutane da dama sun mutu.
An taɓa rikice-rikicen aqeeda tsakaninsa da wasu ƙungiyoyin da’awa, amma shi yana nan a kan hanyar zaman lafiya da jan al’umma zuwa ga Qur’ani da Sunna.
Tsohon shehi ne da Allah ya yi wa tsawon rai; ya shiga shekaru 100s.
Ya bayyana a cikin wata hira cewa yana da ’ya’ya fiye da 60–70 da jikoki masu yawa.
Muna kara rokon ubangiji ya gafarta masa zubansa,
Amin.
REPORTED: Abubakar D. Bature Danbattu
SOURCE: RFI HAUSA
