TURƘASHI: Anyi Nasaran Cire Harsashi 16 a Jikin Wani Dan Najeriya da Asibitoci suka ki Karbarsa

TURƘASHI: Anyi Nasaran Cire Harsashi 16 a Jikin Wani Dan Najeriya da Asibitoci suka ki Karbarsa

 


 

Wani matashi a Najeriya  ya tsallake rijiya da baya an zaro ɓaraguzan harsasai 16 a jikinsa bayan anyi masa tiyata a wani Asibiti dake London.

Sai dai Dangin Kene sun koka kan cewa sun yi ta yawo dashi a Najeriya amma asibitocin ƙasar sun ƙi karɓarsa har sai an kawo rahoton yan sanda, Idan banda Allah ya taimake su sunyi dabarar daukar shi zuwa ƙasar waje (London) ba da ya rasa ransa saboda sakacin Asibitocin Najeriya.




"In sha Allah za a ƙarasa yi masa aiki a cire ragowar harsasai 3 da suka rage, ku taya mu da addu'a" inji dangin Kene

Allah yasa mudace Amin.


SOURCE: Jaridar Ayau

REPORTED BY: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post