Najeriya na Nazarin Mika Harkokin Samar da Wutar Lantarki ga Gwamnatocin Jihohi

Najeriya na Nazarin Mika Harkokin Samar da Wutar Lantarki ga Gwamnatocin Jihohi

 




Gwamnatin Najeriya na nazarin mikawa gwamnatocin jihohi hannayen jarinta a kamfanonin samar da wutar dake fadin kasar, domin sanya ido a kai da kuma tabbatar da cewar ana samun wutar yadda ya dace.

Yanzu haka gwamnatin Najeriya ke rike da kashi 40 na hannayen jarin kamfanonin samar da wutar guda 11 da ake kira DISCO, tun bayan mayar da su a hannun ‘yan kasuwa shekaru 10 da suka shude, yayin da kowanne guda ke samar da wutar a jihohi akalla 3 zuwa sama da haka.

Ministan samar da wutar, Adebayo Adelabu ya bayyana wannan shirin, yayin da yace kofofinsu a bude suke ga gwamnatocin jihohin domin cimma yarjejeniya a kan wannan shirin.



Najeriya mai dauke da yawan mutane sama da miliyan 200, bata iya samarwa jama’arta yawan wutar da suke bukata domin gudanar da harkokin yau da kullum, matsalar da ta tilastawa wasu masana’antu rufewa domin komawa kasashen dake makotaka da kasar.

Wannan matsala ta rashin wutar tafi illa ga masu kananan masana’antu wadanda suka dogara da ita domin gudanar da harkokin su na yau da kullum, a Kokarin gwamnatin da ta shude ta shugaban kasa Muhammadu Buhari na gina tashar samar da wutar Mambilla wadda aka dade ana mahawara a kai ya ci tura, saboda abinda wasu suka kira zagon kasa daga wasu dake adawa da aikin.



Yanzu haka bankin raya kasashen Afirka na AfDB ya ware dala biliyan guda domin bunkasa tashoshin samar da wutar lantarki a wasu kasashen Afirka daga shekara mai zuwa, cikin su harda Najeriya.

Source: Liverty Tvr

Post a Comment

Previous Post Next Post