Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ƙara tabbatar wa gwamnatin Amurka cewa Najeriya na kan turbar da take a kai ta yin riƙo da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.
Ya ce akwai buƙatar wannan ‘yanci sosai domin ta hanyar kafafen yaɗa labarai ne dimokraɗiyya ke ka ƙara karsashi, tasiri da nagarta a cikin a ciki da zukatan al’umma.
Hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Mataimaki Na Musamman a Fannin Yaɗa Labarai ga Minista, Rabiu Ibrahim ya fitar a ƙarshen makon jiya.
Minista Idris ya bayyana haka a lokacin da Babban Jami’in Amurka mai Kula da Al’amurran Nijeriya, Mista David Greene kai masa ziyara cikin makon jiya.
“Yayin da mu ke goyon baya da ɗabbaƙa ‘yancin kafafen yaɗa labarai da na ‘yan jarida, muna kuma yin kira ga gwamnatin Amurka ta ba mu goyon baya ta hanyar ƙara zurfafa horaswa ga ‘yan jarida, musamman a fannin binciken tabbatar da gaskiya, fayyace sahihin labari daga labaran bogi.
Idris ya ce, “yin hakan zai ƙara rage yawan watsa labaran bogi, bayanan karkatar da hankulan jama’a da rage bazuwar ji-ta-ji-ta a cikin jama’a.”
Ministan ya jaddada aniyar da Nijeriya ta sa a gaba wajen ƙara wa dimokraɗiyya daraja da ƙima, ya na mai cewa, “muhimmin abu ne a matsayin Amurka na babbar ƙawar Nijeriya ta ƙara zurfafa goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan.
A jawabin sa, Greene ya ce Amurka na goyon bayan Nijeriya 100 bisa wajen inganta dimokraɗiyya da inganta ayyukan kafafen yaɗa labari, Ya ce domin an keto shekaru da dama ta na bayar da gurabun ƙaro ilmi, bada horaswa da kuma fannin inganta tsaro.