Ƙungiyar ƙasashen Yammacin Afirka, Ecowas ta yi alla-wadai da kokarin hargitsa zaman lafiya a Saliyo, Ecowas a wata sanarwa da ta fitar ta ce abin takaici ne ganin yadda wasu tsiraru mutane suka yi kokari tada hankula da hargitsa zaman lafiya da dokokin kudin tsarin mulkin kasa a Saliyo.
Ƙungiyar ta bukaci a kama tare da gurfanar da wadanda suka aiwatar da wannan yunkuri haramtacce, Gwamnatin Saliyo dai ta sanya dokar hana fita Ta sa'o'i 24 a faɗin ƙasar a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwantar da hankulan mutane
Da safiyar Litinin din da ta gaba ta ne mazauna birnin Saliyo suka ce sun ji ƙarar harbe-harben ne daga aƙalla barikokin soji biyu da ke birnin.
Wani jami'in da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar masa cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun fasa gidan yarin 'Pademba Road' da ke tsakiyar birnin Freetown tare da sakin fursunoni.
Published by: Abubakar D. Bature
Source: Liverty TVR