Hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa FAAN, ta haramtawa fasinjoji amfani da jakar ‘Ghana Must Go’ a dukkan filayen jiragen saman Najeriya.
Wata sanarwa da shugaban hukumar, Henok Gizachew, ya fitar mai taken, ‘Re: Prohibition of Use Of Ghana Must Go’ ta ce haramcin ya shafi fasinjojin da ke bi ta filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Ta ce jakar na haddasa asarar ga kamfanonin jiragen sama tare da lalata na’urar tantance kaya a filayen jiragen.
Published by: Abubakar D. Bature
Tags:
News