Assalamu Alaikum warahmatullah wa barakatuh 'yan uwa barka da yau ina yiwa kowa fatan alkairi, Allah ya sadamu da alkairinsa, A rubutun namu na yau zanyi cikakken bayanine akan yadda ake ajiye numbobi a gmail cikin sauƙi.
Ba iya contact kadai ba zaka iya ajiye photos, videos da files a gmail É—inka sabida kowanne Gmail yanada storage da ya kai 15GB, a wannan 15GB din zaka iya ajiye video, photos, files.
Ajiye numbobi a gmail yanada matuƙar amfani domin idan ka ajiye numbobinka a gmail dinka koda ka rasa sim ko wayarka baki ɗaya, ba zaka rasa numbanka ko ɗaya ba matsawar ba gmail naka ka rasa ba.
Kada rubutun yayi tsayi sosai bara mu shiga bayanin. Hanya biyu zuwa uku ce zaka iya wannan aikin, amma bara mu ɗauki mai sauƙin. Da farko zaka sauke wannan app mai suna Google Contact, zakaga sama da mutum BILLION 1 suke amfani dashi.
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.google.android.contacts
Bayan ka sauke sai ka shiga cikin app din, a kasa zakaga "Fix & Manage" sai ka danna gun, bayan ya buɗe sai ka shiga "Import from SIM" bayan ka danna gun idan sim biyu ne zai baka zaɓi sai ka zabi wanda kakeso kayi copy numbobin nashi, bayan ka zaba zai nunama dukkanin numbobin da suke kan sim ɗin zakaga sunyi Mark duka,
A sama zakaga Gmail da yake kai idan ba gmail ɗaya bane a wayanka sai ka danna sunan Gmail din zai nunama dukkanin gmails da suke kan wayarka sai ka zaɓi Gmail da kakeso kayi save numbers din a cikinsa, a sama zakaga "Import" sai ka danna gun, nan take zakaga numbobin duka sunyi save a gmail naka, shikenan ka kammala.
Written by: Abubakar D. Bature