Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara himma wajen kawo sauyi a kasar, yana mai cewa ƴan Najeriya na son ganin an samu sauyi cikin gaggawa.
Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya kai masa ziyarar ban girma tare da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida a Minna a jiya Lahadi.
A cewar wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, Suleiman Haruna ya fitar, Abubakar ya taya ministan murnar nadin nasa.
Yayin da yake bayyana kwarin gwiwa kan yadda ministan zai iya daga darajar gwamnati a wannan mawuyacin lokaci, Janar din mai ritaya ya ce: “aikin kakaki aiki ne mai wuyar gaske, domin tallata martabar gwamnati a cikin mawuyacin hali.
“Gwamnatin ta fuskanci yanayi mai matukar wahala kuma ta gaji kalubale da dama ta fuskar tattalin arziki, tallafin man fetur, da kuma tsaro.
“’Yan Najeriya, a matsayinsu a al’umma, suna son a samu sauyi cikin gaggawa. Don haka, sakona gare su shi ne su hada kai da gwamnati domin shawo kan wadannan kalubale,” in ji tsohon shugaban Kasar Alhaji Abdussalami Abubakar.
Reported by: Abubakar D. Bature
Source: Daily Nigerian Hausa