Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani

Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani

 



Masarautar Kano ta yi fiye da shekara 2000 da kafuwa, masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa a yammacin Afirka, Tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru - aru tun zamanin jahiliyya kafin zuwan addinin Islama.

Masarautar ta taimaka wajen bunkasa garin
Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya,  Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a  yankin Arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da garin,

Asalin Kalmar "Kano" Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita, Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta,

Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro
kasancewar akwai manyan duwatsu da
tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake
idan an kai musu hari,  Duwatsun su ne dutsen Dala da Goron Dutse da Fanisau da Jigirya da Magwan.

ALSO READ: Tarihin Abubakar Imam Marubucin Magana Jarice Da Nasarorin Dayasamu A Rayuwarsa

Akwai kuma koguna daban-daban da suka
kewaye yankin, da suka hada da kogin
Jakara, da da sauransu, Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama, Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kanau, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano.

Masanin Tarihi Dakta Tijani Muhammad
Naniya ya ce har kawo yanzu masana ba su
kai ga tantance lokacin da aka fara zama a
yankin na Kano ba, Sannan a cewarsa, masana basu gama tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a yankin na Kano ba.

Ya ce akawai Gaya ta Kano da ta Nijar da kuma ta yankin Sakkwato, Babu cikakken bayani kan lokacin da aka fara zama a yankin Kano, amma a cewar Dakta Naniya an taba gano wata makera a kusa da dutsen Dala da masana suka ce ta kai shekara 200 bayan Haihuwar Annabi lsa, Hakan ya sa ake hasashen cewa garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin addinin musulunci, Ma'ana a yanzu birin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.

Sarautar Kano A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa, Jama'ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su, Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutanen, inda daga nan ne aka fara samun canje - canjen sarakuna tun daga maguzawa harzuwa fulani wadanda haryanzu suke rike da masarautar wanda hanzu haka Alh Aminu Ado Bayero ke zaman sarki Na 15 a jerin sarakunan fulani.

Post a Comment

Previous Post Next Post