A tsawon shekara hudu na mulkin Gwamna Rimi, Kano ta ga abubuwan ci gaba da abubuwan tarihi da ba za a manta da su ba, Gwamnatinsa ce ta fara kirkiro sabuwar ma'aikatar raya karkara da ta taimaka wajen gina karkarorin Jihar da babu wata Gwamnati a baya da ta yi.
Shi ne ya kafa hukumar ba da wutar lantarki da aka kai kauyuka da karkara kusan 60, ya gina wajen ba da ruwa sama da 91 da gina hanyoyin karkara masu tarin yawa, Gwamnatin Rimi ce ta gina kananan asibitoci sama da 15 da babban asibitin kwanciya a garin Bichi.
A bangaren sarauta kuwa ya daukaka darajar kananan hakiman Rano, Gaya da dutse masu daraja ta daya, ya kirkiro sababbin kananan hukumomi har guda tara.
Gwamnatin Rimi ta gina sabuwar makarantar jiyya da Ungozoma da ke unguwar Gyadi - Gyadi, Haka kuma shi ne ya kafa amfanin gona da inganta shi ta "KNARDA" da kafa Kamfanin sayar da kayan noma na " KASCO" Shi ne ya kafa gidan telebijin na Jiha CTB 67 da gidan jaridar Jiha ta "TRIUMPH".
A zamanin Gwamna Rimi, Kano ta ga musibar Muhammadu Marwa Mai tatsine, wani Malami dan ta adda da ya yi ta yanka jama'a, wanda sai da sojoji suka kawo dauki kafin a ga karshensa.
A shekarar 1981, bayan da rigimar cikin gida ta P.R.P. ta yi tsamarı, mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Ibraim B.B. Farouk ya ki goyon bayan bangaren Gwamnan.
Wannan ta jawo tsige shi da majalisar Jihar
Kano ta yi, sannan Aka nada dan Dawakin - Tofa, Alhaji Audu Dawakin Tofa a matsayin sabon mataimakin Gwamna.
Alhaji Muhammad Abubakar Rimi ya rasu a ranar lahadi wanda yayi dai dai da 4/4/2010 anyi jana'izar sa kamar yadda Addinin musulunci ya tanada.