Mataki na Farko Ne Wannan, a na Biyun Wallahi Ba sani ba Sabo - Hisbah ga yan Kannywood

Mataki na Farko Ne Wannan, a na Biyun Wallahi Ba sani ba Sabo - Hisbah ga yan Kannywood

 



Hukuma mai umarni bisa aikata kyakykyawan aiki da kuma hani bisa aikata mummuna (Hisbah) ta jihar Kano, ta yabawa yan masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, wadanda suka amsa gayyatar da tayi musu a ranar Litinin, inda ta nemi hadin kansu akan tsaftace harkokin fim a fadin jihar Kano, musamman yadda ake aikata wasu abubuwa da suka ci karo da shari'ar musulunci a cikin wasu finafinai.

Babban kwamandan hukumar, Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin ganawarsa da yan Kannywood, inda yace sun gayyato su ne akan yadda yara Mata ke zuwa Kano daga wasu Jihohi ko wasu ƙasashe da nufin shiga fim, amma sai su kama Daki su na aikata abinda ba shikenan ba, saboda haka Hisbah ke so duk yarinyar da tazo irin wannan a kawo mata ita.




Har ila yau, Daurawa yayi magana akan yadda ake nuna jarumi ya fito a Liman yana jan aya ko Hadisi ko fassarawa ba daidai ba, saboda Hisbah zata bada wakili da zai dinga duba irin wannan, da kuma yadda ake sanya suna mai asali a Addini da wata mummunar dabi'a a cikin fim, harma ya bada misali da sunan "Mahmud" da aka sakawa wani jarumi a wani fim, amma yana aikata dabi'u marasa kyau, wanda shi da kansa ya nemi wanda yake É—aukar nauyin haska fim din, ya nemi da ya daina daukar nauyi har sai an gyara abin.




Daurawa ya ja kunnen wadanda suke ganin kamar sun fi ƙarfin doka, inda yace su daina tunanin haka, don wani yana taƙama da cewa yana da sanayya da wasu manyan yan siyasa saboda haka ba zasu fara doka tayi aiki a kansa ba, to wannan ragon tunani ne, domin an basu wannan mukami ne don su yiwa Addinin musulunci aiki, kuma shi suke yi.

Bugu da ƙari, Daurawa yace sun sha gayyato jarumai su nusar dasu kuskuren da suke aikatawa a fim, amma jaruman suna cewa ba laifinsu bane, laifin Daraktoci ne da Furodusoshi, domin bisa umarnin su ake yin furuci, sanya sutura da dabi'a a cikin fim, wannan yasa Hisbah ta ke neman goyon bayan kowanne dan masana'antar Kannywood domin a tsaftace harkokin fim a Kano


Published by: Abubakar D. Bature

Source: Nasara Radio

Post a Comment

Previous Post Next Post