Jarumi Abdallah Amdaz ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa

Jarumi Abdallah Amdaz ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa

 



Jarumi kuma mawaƙi a masana'antar Kannywood, Abdallah Amdaz, ya fara fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa, inda wasu ke ikirarin cewa ya bata musu suna, don haka zasu daina saka shi a fim, harma wasu na barazanar gurfanar dashi a gaban Shari'a. 




Also Read: Mataki na Farko Ne Wannan, a na Biyun Wallahi Ba sani ba Sabo - Hisbah ga yan Kannywood

A ranar Litinin ne Abdallah Amdaz ya bayyana wasu dabi'u marasa kyau da wasu yan masana'antar ke aikatawa, a wajen taron da hukumar Hisbah karkashin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta shirya da yan Kannywood. 

Sai dai jarumin yace ya bayyana abubuwan da ya fada ne saboda yadda Daurawa yace su fadi tsakaninsu da Allah akan matsalolin da suke so a gyara, wanda yace shi kuma yana ganin yan fim yan uwansa ne, bai kamata su je lahira su na la'antar junansu ba, gwara tun a Duniya ya bayyana gaskiya, tunda dai Abincinsa da ɗaukakarsa na hannun Allah.




Post a Comment

Previous Post Next Post