Sannan ya Kara da cewa.
1. Siyasa Mugun Wasa Inji Margayi Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano ka yarda cewar ita ce arzikinka, sunanka wawa.
2. Idan ka daina Sana’a ka rungumeta, kayi babbar wauta.
3. Cikakkiyar makauniyace ba ta san mai wahalta mata ba, da murya ta ke amfani.
4. Idan ta tashi yi maka tutsu sai ka zabi makiyinka da hannunka.
5. Idan kaci mutuncin wani saboda ita, kayi babbar wauta, domin zata kunyataka wata Rana.
6. Ba kasafai ta ke rike amanar da ka bata ba, tafi komai cin Amana.
7. Idan ka biye Mata kaci mutuncin Dan uwanka, babu shakka Sai ka yi da nasani wata rana.
8. Tafi kwaya da sholisho kashe zuciya, kada ka yarda ta kashe maka zuciya.
9. Yadda ka ga Dan Jaki haka take, duk sanda ta tashi yin harbi yi za tayi, domin haka ka yi taka tsantsan da ita.
10. Duk runtsi ka da ka sake ka manta da wanda ya mutuntaka a cikinta, Koda ya munana maka daga baya.
11. Tafi chacha kwadaita maka igiyar zato, kayi kokari ka san haka.
12. Ta nada mugwaye da nagartattun 'ya’ya, domin haka ka san da wanda za kayi mu'amala.
13. Shaidaniyace ta gaske, yadda ka ga Shaidan haka take da zuga, idan ta wullaka wani ramin sai an rasa mai tsamoka.
14. Kabita sannu a HANKALI kada ka yi Mata garaje, akwai wawaye acikinta sai su yi maka wauta, har ila yau akwai nagartattun mutane a cikinta ka daure ka rabe su.
15. Ka da ka sake ka bata dukkan karfinka, domin idan karfinka ya qare ba zata iya tagaza maka ba.
16. Ka da ka rama dukkan zagin da za’a yi maka a cikinta, sannan ka da ka sake ka kalli wanda ya kulla maka sharri a cikinta, domin sharri Dan aike ne, komai tsawon zamani zai dawo.
17. ka da kaji tsoro ko shakkar wani Danta, arziki da lafiya ko rayuwarka duk suna hannun Allah ne.
A Karshe mubi siyasa a sannu, a hankali saboda tafi komai dadi kuma tafi komai wahala mubi komai sannu a hankali wata Rana Sai labarina.
Inji marigayi Yusuf Maitama sule.
Allah ya gafarta masa yayi Mai rahama Amin.
Reported by: Abubakar D. Bature