'Yan Siyasa Ne Ke Magudin Zabe Ba Muba - INEC

'Yan Siyasa Ne Ke Magudin Zabe Ba Muba - INEC

 



Sabuwar Kwamishinar ZaÉ“e ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi ce ta bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula, (CSOs) Sannan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ba za ta bari a yi maguÉ—in zaÉ“e a babban zabe mai zuwa na 2023 ba domin daman ba halinta ba ne.

A cewarta, maguɗin zaɓe zai yi matukar wahala domin hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da sahihin zabe, Mrs Ugochi ta ce, INEC ba za ta taba yin magudin zabe ba. Ƴan siyasa ne ke tafka magudin zaɓe, amma za mu yi iya gwargwadon abin da za mu iya wajen daƙile maguɗin zaɓe.

Tsarin da muka fito dashi yanzu ya sanya maguÉ—in zaÉ“en zai yi na matukar wahala. Idan kuna son yin magudi a yanzu muna da BVAS. Shin ta hanyar satar hanya ta BVAS ne ko kuma kulle rumbun ajiye bayanai  inda komai ya ke, yanzu yana da wahala sosai.

Wannan lokaci ne da kafafen yada labarai da CSOs za su yi aiki tukuru da kuma wayar da kan jama’a. Mu ba ma nuÆ™u-nuÆ™u za mu yi iya kokarinmu a duk abin da muke yi. Za mu tsaya tsayin daka domin tare duk wani hari daga waje. Ya kamata kafafen yada labarai su ba mu goyon baya don kada mu samu matsaloli a abin da muka sa a gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post