Iyayen dalibin nan na Jami’ar Tarayya da ke Dutse ta jihar Jigawa a Nijeria, Aminu Azare, sun roki uwar gidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari da ta yi wa Allah da Girman Annabinsa, ta yi hakuri ta bari a sake shi.
An dai kama dalibin ne wanda ke ajin karshe a jami’ar sakamakon rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana bayyana uwargidan shugaban kasar a matsayin wadda ta ci kudin talakawa ta yi bulbul tare da hada hotanta da rubutun nasa.
Inda bayan kwana biyu da wallafa wannan rubutun ake zargin hukumar tsaro ta farin kaya tayi awon gaba dashi, kawo yanzu babu wani takamammen Mutun Wanda zai iya baka tabbacin Inda wannan Bawan Allah yake.
A wata zantawa wani ɗan uwan matashin, Shehu Baba Azare ya ce tsare Muhammed ɗin ya jefa danginsu a cikin damuwa, ya roƙi Aisha Buhari da ta yi hakuri ta yafe masa a matsayin ta na uwa ga ƴan ƙasa. Sai dai kuma har yanzu ofishin Mai ɗakin shugaban ƙasa ba su ce komai a kan lamarin ba.