Shugaban Russia Vladimir Putin ya umurci
kwamandojin sojin kasar su shirya sojojin Russia masu kula da makaman nukiliya su kasance cikin shiri.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa a fadar Kremlin wanda ministan tsaro da kwamandan sojojin kasar suka halarta.
Mista Putin ya ce manyan jami'an kasashen yammaci sun yi kalamai masu zafi kan Russia.
Ya kira takunkuman da kasashen yammaci suka kakabawa kasarsa a matsayin haramtattu.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida da suka makale a Ukraine da ke fuskantar hare-hare daga dakarun sojin Russia.
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da wakilan ma’aikatarsa suka yi da Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Femi Gbajabiamila a ranar Litinin.
A wani sako da Ofishin Kakakin Majalisar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnati za ta fara aikin dawo da ’yan kasarta gida Najeriya daga ranar Laraba.
Ministan ya ce Najeriya ta kammala duk wasu shirye-shiryen dawo da ’yan kasarta gida wadanda suka makale a wasu kasashen saboda yakin Rasha da Ukraine.
“Muna fatan fara jigilar dawo da su gida ranar Laraba, muna aiki ba dare da rana don tabbatar da ranar Laraba mai zuwa mun tura jirgi ya debo su.”
Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da aniyarta na soma dawo da ’yan Najeriya gida daga kasar Ukraine biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.
Gwamnati ta dauki azamar gudanar da wata jigilar jiragen sama ta musamman domin kwaso yan kasarta daga Ukraine sakamakon yadda rikici ke kara ta’azzara tsakanin kasar da Rasha.
Ministan Harkokin Wajen Kasar, Geoffery Onyeama a wata hirarsa da gidan talabijin na NTA, ya ce an tuntubi Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Kiev domin soma jigilar wadanda ke son dawowa gida Najeriya.
Sannan sama da mutune milliyon dari ne "yan ainayin kasar ukraine suka yi hijira izuwa Makotan kasar.