A cigaba da rusau da gwamnatin jihar kano karkashin Engr. Abba K. Yusuf keyi Na Filayen da gwamnatin da ta gabata ta siyar An gano wata plaza mai hawa biyu da kuma gidan kasa dake masallacin Idi wadda mutane ke jita jitan giya ake boye wa aciki.
Wannan lamari ya biyo bayan da samari masu cin ganima suka fasa ginin suna cire rodina yayin fasa daben gurin ke da wuya suka ga ramin gidan kasan.
Wannan gini ya kasan ce yana kallon masallacin isyaka rabi'u dake kofar mata kuma ginin da daya daga cikin gine ginen da ba'a rushe da wuri ba, mutane da dama nayin cin cirindo wajen zuwa gane wa idonsu.
Lamarin ya karade kafafen sada zumunta inda kowa ke fadar albarkacin bakinsa. Mudai ba ibin da zamu ce sai Allah ya kyauta.
Reported: Abubakar D. Bature