Kudin Inshorar Ababen Hawa Yayi Tashin Gwauran Zabi | NAICOM

Kudin Inshorar Ababen Hawa Yayi Tashin Gwauran Zabi | NAICOM


Sanarwar na ƙunshe ne a cikin takarda mai lamba NAICOM/DPR/CIR/46/2022 ga kamfanonin inshora, mai dauke da kwanan wata Disamba 22, 2022, Hukumar Inshora ta Kasa, NAICOM, ta kara kudin inshorar masu ababen hawa daga N5,000 zuwa N15,000 duk shekara daga Janairu 2023.

Anyi wa sanarwar lakabi da Sabon Farashi mai girma na Inshorar Motoci, kuma daraktan Manufofi da Dokoki na NAICOM, Leo Akah ne ya sanya hannu a madadin Kwamishinan Inshorar.

Bisa aiwatar da aikinta na amincewa da kimar kuɗin inshora a ƙarƙashin sashe na 7 na Dokar NAICOM ta 1997 da sauran dokoki, Hukumar ta fitar da wannan da'irar akan sabon farashin inshorar motoci wanda zai fara aiki daga 1 ga watan, Janairu 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post